chat

SIFFAR SALLAR ANNABI – TSIRA DA AMINCIJ ALLAH

SIFFAR SALLAR ANNABI – TSIRA DA AMINCIJ ALLAH

SIFFAR SALLAR ANNABI – TSIRA DA AMINCIJ ALLAH

Raba:

 SU TABBATA AGARE SHI - Na shehin Malami AbdulAziz ɗan Abdullah ɗan Baaz Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin ƙai Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah Shi kaɗai, tsira da aminci su tabbata ga bawanSa kuma manzonSa Annabimmu Muhammad da alayansa da sahabbansa. Bayan haka: Waɗannan wasu taƙaitattun bayanai ne a cikin siffar sallar Annabi, ina son in gabatar da su ga dukkanin musulmi da musulma, domin duk wanda ya gani yayi ƙoƙarin koyi da shi a cikin hakan, saboda faɗinsa: (Ku yi sallah kamar yadda kuka ga ina yin sallah) 1 Bukhari ne ya rawaito shi. Ga bayanin hakan ga mai karatu: 1 Bukhari, babin kiran sallah (605), Darimi, al-Sallah: (1253). 3

Kyautata alwala 1. Zai kyautata alwala, shi ne yayi alwala kamar yadda Allah Ya umarce shi, don yin aiki da faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -:

 {Ya ku waɗanda suka yi imani, idan kun tashi za ku yi sallah, to, ku wanke fuskokinku da hannayenku zuwa gwiwoyi, kuma ku shafi kawunanku, kuma (ku wanke) ƙafafunku zuwa idon sawu}2 Zuwa ƙarshen ayar. Da faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi _ (Ba’a karɓar sallah ba tare da tsarki ba)3 . Fuskantar Alƙibla 2- Wanda zaiyi sallah zai fuskanci alƙibla, ita ce kuma Ka’abah, duk ta inda yake da dukkanin jikinsa yana nufin yin sallar da zaiyita da zuciyarsa ta farilla ko nafila, ba zai furta niyya da harshensa ba, domin ba a shar’anta furta niyya ba, yin hakan bidi’a  ne, saboda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai furta niyya ba haka nan sahabbansa - Allah Ya   2  Suratul Ma'idah, aya ta: 6. 3  Muslim, Tsarki (224), Tirmizi, Tsarki (1), Ibnu Majah, Tsarki da sunnoninsa (272), Ahmad (2/73). yarda da su -, sai ya sanya suturar da zai yi sallah ga reta idan ya kasance liman ne ko shi kaɗai yake sallah. Fuskantar alƙibla sharaɗi ne a sallah, saidai a wasu mas’alolin da aka togance kuma sanannu da a ka yi bayaninsu a littattafan malamai. Kabbarar harama, da ɗaga hannaye biyu a lokacin kabbarar, da kuma ɗora hannayen biyu akan ƙirji. 3. Yana yin kabbarar harama yana cewa: Allahu Akbar, yana mai kallon inda zai yi sujjada da idanuwansa zuwa bigiren sujjadarsa. 4. Yana daga hannuwansa daura da kafaɗunsa ko daidai da kunnuwansa. 5. Ya sanya hannuwansa a ƙirjinsa, na dama akan tafin na hagu, da wuyan hannu da damtse, saboda tabbatuwar hakan daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. Addu'ar buɗe Salla 6. An sunnanta, (mai sallah) ya karanta Addu’ar buɗe sallah, ita ce: Ya Allah Ka nisantar da tsakanina da kurakuraina kamar yadda Ka nisantar da gabas da yamma, Ya Ubangiji Ka tsaftace ni daga kurakuraina kamar yadda ake tsaftace farin tufa daga datti, ya Allah 5 Ka wankeni daga kurakuraina da ruwa da ƙanƙara da sanyi. Idan (mai sallah) ya ga dama maimakon wannan sai ya karanta: Tsarki ya tabbata a gareKa ya Allah haɗi da gode maKa, (4). 4  kuma sunanKa ya girmama kuma ƙarfinKa ya ɗaukaka, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Kai Idan ya yi (wata addu’ar) da ba waɗannan ba cikin addu’oin buɗe sallah tabbatattu daga Annabi to babu wani laifi, abinda yafi yayi wannan wani lokacin kuma yayi waccan wani lokacin daban, domin hakan yafi kaiwa ƙoli wurin biyayya, sannan sai ya ce: Ina neman tsari daga sheɗan jefaffe. Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai, sai ya karanta Fatiha, saboda faɗinSa: (Babu sallah ga wanda bai karanta Fatihatul Kitab ba)5 . Sai ya ce: Amin, bayan (ya karanta ta) a bayyane a cikin sallar da ake karatu a bayya ne,  kuma a sirrance idan sallar a ɓoye ake yinta, sannan ya karanta abinda ya sawwaƙa na AlKur’ani. 4 Al-Bukhari, Kiran sallah (711), Muslim Masallatai da wuraran sallah (598), Nasa’i buɗe sallah (895), Abu Dawud Sallah (781), Ibnu Majah, Iƙamatus Salah Wassunnantu fiha (805), Ahmad (2/231), al-Darimi (Sallah1244). 5 Bukhari Kiran sallah (723), Muslim (394), Tirmizi Sallah (247), Nasa’i Buɗe sallah (911), Abu Dawud Sallah (822), Ibnu Majah, Iƙamatus Salah Wassunnantu fiha (837), Ahmad (5/316), al-Darimi (1242). 6 Abinda ya fi ya karanta bayan Fatiha a sallar Azahar da La’asar da Issha cikin tsakatsakin Mufassal, a Asuba cikin dogayan Mufassal, a Magariba kuma wani lokacin cikin dogayan Mufassal, wani lokacin kuma cikin gajerun Mufassal, don yin aiki da hadisan da suka zo da hakan . Ruku’i da tasowa daga ruku’in da kuma abinda ya ƙunsa 7. Zai yi ruku’i yana mai yin kabbara kuma yana ɗaga hannayansa zuwa daidai kafaɗunsa ko kunnuwansa, yana mai sanya kansa daidai da gadon bayansa, yana ɗora hannayansa akan gwiwowinsa, yana mai wara yatsunsa, ya kuma nutsu a ruku’insa yana mai cewa: Tsarki ya tabbata ga Ubangijina Mai girma.   Abinda yafi shine ya maimaita faɗin sau uku ko sama da haka, kuma an so ya ce tare da hakan: (Tsarki ya tabbata a gareKa ya Allah Ubangiji tare da gode maKa, ya Ubangiji Ka gafarta min6 . 8. Yana ɗago kansa daga ruku’i yana mai ɗaga hannayansa zuwa kafaɗunsa ko daura da kunnuwansa, 6 Bukhari Tafsirul Kur’an (4683), Muslim Sallah (484), Nasa’i Taɗbik (1122), Abu Dawud (877), Ibnu Majah Iƙamatus Salah Wassunnatu fiha (889). 7 yana mai cewa: (Allah Ya ji mai gode masa (7) -7 Idan ya kasance liman ko shi kaɗi ne sai ya ce a lokacin da yake tasowa: (Rabbana Walakal Hamdu, Hamdan Kasiran Ɗayyiban Mubarakan Fihi, Mil’as Samawati, Wa Mil al’ard, Wa Mil’a Ma Baina huma, Wa Mil’a Ma Shi’ata Min Shai’in Ba’adu) 8 . Amma idan ya kasance mamu ne to a lokacin ɗagowa daga ruku'u sai ya ce: Rabbana walakal Hamd”. Zuwa ƙarshen abinda ya gabata, idan kuma kowannan su ya ƙara, wato liman da mamu da mai sallah shi kaɗai" (Ahlus Thana’i wal majd, a haƙƙun ma ƙalal abdu, wakulluna laka abdu. Allahumma La mani’a lima aaɗaita wala mu’uɗiya lima mana’a ta, wala yanfa’u zal jadd mikal jadd (9)"9 Yin hakan yana da kyau, saboda tabbatuwar hakan daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma an so kowannen su ya ɗora hannuwansa a ƙirjinsa kamar yadda yayi a tsaye kafin yayi ruku’i, saboda tabbatuwar abinda yake nuni akan hakan daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cikin Hadisin Wa’il ɗan Hujri da Sahl ɗan Sa’ad - Allah Ya yarda da su -. 7 Bukhari, Azan (657), Muslim al-Sallah (411), Tirmizi al-Sallah (361), Nasa’i Imamah (832), Abu Dawud Sallah (601), Ibnu Majah Iƙamatus Salah Wassunnatu fiha (1238), Malik Annida’u Lissalah (306), Darimi al-Sallah (1256). 8 Muslim, Salatul Musafirin wa ƙasriha (771), Tirmizi al-Da’awat (3423), Abu Dawud al-Sallah (760), Ahmad (1/103). 9 Muslim Sallah (477), Nasa’i Taɗbiƙ (1068), Abu Dawud Sallah (847), Ahmad (3/87), Darimi Sallah (1313). 8 Sujjada da ɗagowa daga gareta da abinda ya ƙunshi hakan 9. Yana yin sujjada tare da kabbara, yana sanya gwiwowinsa kafin hannayansa, idan haka ya sawwaƙa a gare shi, idan kuma yayi masa wahala sai ya fara gabatar da hannayansa kafin gwiwowinsa, yana mai fuskantar da yatsun kafafuwansa da hannayansa zuwa alƙibla, yana mai haɗe yatsun hannuwansa yana miƙar da su, kuma sujjudar ta kasance akan gaɓɓai bakwai: Fuska tare da hanci, da hannuwa da gwiwowi, da cikin yatsun ƙafafuwa, kuma ya ce: Subhana Rabbiyal Aalah.   ) ( �ﻋﻷا �ر نﺎﺤ�ﺳ) An sunnanta ya faɗi hakan sau uku ko sama da haka , kuma an so ya faɗa tare da hakan: (Subhana Kallahumma wabi hamdiKa, Allahumma ghfirli 10 . Ya yawaita addu’a saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: (Amma a ruku’i to ku girmama Ubangiji a cikinsa, Amma a Sujjada to ku yi ƙoƙarin addu’a domin ya cancanci a amsa muku) 11 Ya kuma roƙi Ubangijinsa na alhairan duniya da lahira, hakan a sallar farilla ne ko sallar nafila, ya buɗa damatsansa daga ɓarin jikinsa, cikinsa kuma daga 10 Bukhari, Azan (761), Muslim, Sallah (484), Nasa’i Taɗbiƙ (1122), Abu Dawud, Sallah (877), Ibnu Majah Iƙamatus Salah Was Sunanu fiha (889), Ahmad (6/43). 11 Muslim (479), Nasa’i Taɗbiƙ (1120), Abu Dawud Sallah (876), Ahmad (1/219), Darimi Assalah (1325). 9 cinyoyinsa, ya kuma raba cinyoyinsa da ƙwaurinsa, ya ɗaga hannayansa daga barin ƙasa, saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare - shi: (Ku daidaita a sujjada, kada ɗayanku ya shinfiɗa hannuwa irin shinfiɗawar kare) 12 Zama tsakanin sujjadu biyu da kaifiyyarsa 10. Yana ɗago kansa tare da kabbara, ya kuma shinfiɗa diddigensa na hagu sai ya zauna a kansa, ya kuma kafe ƙafarsa ta dama, ya ɗora hannayansa akan cinyoyinsa da gwiwowinsa sai ya ce: (Ya Allah Ka gafarta mini Ka ji ƙaina Ka shiryar da ni Ka azurtani Ka tsare ni Ka agaza mini 13 Ya kuma natsu a wannan zaman. 11. Yana yin sujjada ta biyu tare da kabbara, ya kuma yi hakan kamar yadda yayi a sujjada ta farko. 12- Yana ɗago kansa tare da kabbara, sai ya zauna zama ƙanƙani kamar yadda ya zauna tsakanin sujjada biyu, ana kiransa da zaman hutu, wannan zaman mustahabbi ne, idan ya bari babu wani laifi akansa, babu wani zikiri ko wata addu’a a cikinsa, sannan ya yunƙura ya tashi tsaye zuwa raka’a ta biyu yana mai dogara akan gwiwowinsa idan hakan ya yiwu a gare 12 Bukhari Azan (788), Muslim Salah (493), Ahmad (3/192). 13 Tirmizi sallah (284), Abu Dawud Sallah (850), Ibnu Majah Iƙamatus Salah Wassunnatu fiha (898). 10 shi, idan kuma yayi masa wahala ya dogara akan ƙasa, sannan ya karanta Fatiha da abinda ya sawwaƙa a gare shi na AlKur’ani bayan Fatihar, sannan ya yi kamar yadda ya yi a raka’a ta farko. Zama domin yin Tahiya a zama na biyu da kaifiyyarsa 13. Idan sallar ta kasance mai raka’a biyu ce kamar sallar Asuba da Juma’a da Idi biyu, to sai ya zauna bayan ya ɗago kansa daga sujjada ta biyu yana mai kafa ƙafarsa ta dama yana kuma shinfiɗa ƙafarsa ta hagu, yana ɗora hannun sa na dama akan cinyarsa ta dama, yana naɗe yatsunsu baki ɗaya sai manuniya, sai ya yi nuni da ita akan Tauhidi, idan ya naɗe ƙaramin yatsansa da wanda yake biye da shi na dama ya kuma lanƙwasa babban yatsa da na tsakiya ya yi nuni da manuniya (kaɗai) hakan ma ya yi kyau, saboda tabbatuwar duka siffofin biyu daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, abinda ya fi shi ne ya yi wannan a wani lokaci kuma ya yi wancan, sai ya dora hannun sa na hagu akan cinyarsa ta hagu da gwiwarsa, sannan sai ya yi Tahiya a wannan zaman, ita ce kuma: (Dukkanin gaisuwa kyawawa sun tabbata ga Allah, da salloli da kyawawan (maganganu), aminci ya tabbata a gareka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa, aminci ya tabbata a garemu da kuma bayin Allah salihai, ina shaidawa babu abin 11 bautawa da cancanta sai Allah kuma ina shaidawa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne.   Sannan sai ya ce: Ya Allah Ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da iyalan Muhammad kamar yadda Ka yi salati ga (annabi) Ibrahim da iyalan Ibrahim, lalle Kai abin godewa ne kuma mai girma. Ya Allah ka yi albarka ga (annabi) Muhammad da iyalan Muhammad kamar yadda ka yi albarka ga (annabi) Ibrahim da iyalan Ibrahim lalle Kai abin godewa ne kuma Mai girma. 14 Kuma ya nemi tsarin Allah akan abubuwa huɗu, sai ya ce: Ya Ubangiji ina neman tsarinKa daga azabar Jahannama da azabar ƙabari da fitinar rayuwa da ta mutuwa da fitinar Masihul Dajjal (Jujal) 15 Sannan ya yi addu’a da abinda ya ga dama na alhairan duniya da lahira, idan kuma ya yi addu’a ga iyayansa ko wasu daga cikin musulmai duka babu laifi, daidai ne hakan a sallar farilla ne ko nafila, saboda gamewar faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin Hadisin ɗan Mas’ud a lokacin daya koyar da shi Tahiya, sannan ya zaɓi addu’ar da tafi ƙayatar da shi sai yayi addu'a da ita. A wani lafazin kuma, sannan ya zaɓi abinda yake so ya 14 ( )Bukhari, Kiran sallah (797), Muslim Salah (402), Tirmizi Nikah (1105), Nasa’i Sahwu (1298), Abu Dawud Sallah (968), Ibnu Majah, Iƙamatus Salah Wassunnantu fiha (889), Ahmad (1/428), Darimi (1340). 15Bukhari Jana’iza (1311), Muslim Masajid wa mawadi’us Salah (588), Tirmizi Da’awar (3604), Nasa’i Isti’aza (5513), Abu Dawud Salah (983), Ibnu Majah Iƙamatus Salah Wassunnatu fiha (909), Ahmad (2/454), Darimi Salah (1344). 12 roƙa, wannan ya game duk abinda bawa yake so na duniya da lahira, sannan yayi sallama a damar sa da kuma hagunsa, ya ce: Assalamu alaikum wa rahmatullah.   Zama domin yin Tahiya a sallah mai raka’a biyu ko huɗu da kaifiyyarsa Idan sallar ta kasance mai raka’a uku ce, kamar Magariba ko mai raka’a huɗu ce kamar Azahar da La’asar da Issha, sai ya yi Tahiyar da aka ambata a baya, tare da yin salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sannan sai ya yunƙura ya tashi tsaye yana mai dogara a kan gwiwowinsa yana ɗaga hannayansa daidai kafaɗunsa ko daidai kunnuwansa yana cewa: Allahu Akbar, yana mai ɗora hannayansa akan ƙirjinsa kamar yadda ya gabata, sai ya karanta Fatiha kaɗai, idan ya karanta a raka’a ta uku da ta huɗu a Azahar ƙari akan Fatihar a wasu lokutan to babu laifi, saboda tabbatuwar abinda yake nuni akan hakan daga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cikin Hadisin Abu Sa’idu, sannan sai ya yi Tahiya bayan raka’a ta uku a magariba, da kuma bayan raka’a ta huɗu a Azahar da La’asar da isha kamar yadda ya gabata a hakan a sallah mai raka’a biyu, sannan ya yi sallama a damansa da kuma hagunsa, ya kuma nemi gafarar Allah sau uku, sannan ya ce: (Ya Allah Kai ne aminci, daga gareKa aminci yake 13 alherinKa ya yawaita ya Ma’abocin girma da karamci) 16 Kafin ya juya ya fuskanci mutane idan ya kasance liman ne, sannan ya ce: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kaɗai Yake, ba Shi da abokin tarayya, kuma Shi Mai iko ne akan dukkan komai. Ya Allah babu mai hana abinda Ka bayar kuma babu mai bayar da abinda Ka hana, wadatar mai wadata bata anfani a wurinKa, babu ƙarfi kuma babu wata dabara sai da taimakon Allah. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ba ma bautawa kowa sai Shi, ni’ima ta sa ce da falala, da yabo mai kyau, babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, muna masu tsarkake addini gare Shi, ko da kafirai sun ƙi 17 , Sai ya yi tasbihi: Subhanallah, talatin da uku, ya gode maSa kwatankwacin  hakan,  yayi  maSa kabbara kwatankwacin hakan a cikon na ɗarin sai yace: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ba Shi da bokin tarayya, mulki naSa ne, kuma godiya taSa ce, kuma Shi Mai iko ne akan dukkan komai. Kuma ya karanta Ayatul Kursiyy, da Kulhuwa da Falaƙi da Nas a bayan kowacce sallah, kuma an so a maimaita waɗannan surorin uku, sau uku bayan sallar Asuba da Magariba, saboda Hadisan da suka zo akan 16Muslim Masallatai da wuraran sallah(591), Tirmizi Sallah(300), Abu Dawud (1512), Ibnu Majah Iƙamatus Salah Wassunnatu fiha (928), Ahmad (5/280), Darimi Sallah (1348). 17 Bukhari, Kiran Sallah (808), Muslim, Msallatai da wuraran sallah(593), Nasa’i Rafkannuwa (1341), Abu Dawud Sallah (1505), Ahmad (4/250), Darimi Sallah (1349). 14 haka daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. Dukkanin waɗannan zikiran sunna ne ba wajibi ba ne. Kuma an shar’anta ga kowanne musulmi da musulma yin sallah (nafila) kafin sallar Azahar raka’a huɗu bayanta kuma raka’a biyu, da raka'a biyu bayan Magariba, da raka'a biyu bayan sallar Issha, da raka'a biyu kafin sallar Asuba, idan aka haɗa ya kama raka’a goma sha biyu. Waɗannan raka’o'in ana kiransu da Rawatib, domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana kiyaye su a halin zaman gida. Amma a halin tafiya ya kasance ba ya yinsu saidai na kafin Asuba da Wuturi, domin tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana kiyaye su a halin zaman gida da kuma tafiya. farilla18  Abinda yafi a sallaci waɗannan nafilfilin da Wuturi a gida, idan yayi su a masallaci babu wani laifi, saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: “Mafificin sallar mutum a gidansa saidai (sallar) Kiyaye waɗannan raka’oin yana cikin sabubban shiga aljanna, saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: (Wanda ya yi sallah raka’a 18Bukhari, Ladubba (5762), Muslim, Salatul musafirin wa ƙasruha (781), Tirmizi Sallah (450), Nasa’i tsayuwar dare da nafilar rana (1599), Abu Dawud Sallah (1447), Ahmad (5/186), Malik, Kiran Sallah (293), Darimi Sallah (1366). 15 goma sha biyu a yini da dare domin neman lada, Allah Zai gina masa gida a aljanna)19 . Muslim ne ya ruwaito shi a Sahihinsa, idan ya yi raka’a huɗu kafin La’asar, da raka’a biyu kafin Magariba, da raka’a biyu kafin Issha to ya yi kyau, domin abinda yake nuni akan hakan ya inganta daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. Allah Shi ne Majiɓincin datarwa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabimmu Muhammad ɗan Abdullah da alayansa da sahabbansa da mabiyansa da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.  19Muslim Salatul musafirin wa ƙasruha (728), Tirmizi Sallah (415), Nasa’i Kiyamul Lail wa Taɗawwu’un Nahar (1801), Abu Dawud Sallah (1250), Ibnu Majah, Iƙamatus Salah Wassunnatu fiha (1141), Ahmad (6/327). 16

Teburin bayani Kyautata alwala ............................................................... 4 Fuskantar Alƙibla ............................................................. 4 Kabbarar harama, da ɗaga hannaye biyu a lokacin kabbarar, da kuma ɗora hannayen biyu akan ƙirji. ........ 5 Addu'ar buɗe Salla .......................................................... 5 Ruku’i da tasowa daga ruku’in da kuma abinda ya ƙunsa ............................................................................... 7 Sujjada da ɗagowa daga gareta da abinda ya ƙunshi hakan .............................................................................. 9 Zama tsakanin sujjadu biyu da kaifiyyarsa.................... 10 Zama domin yin Tahiya a zama na biyu da kaifiyyarsa . 11 Zama domin yin Tahiya a sallah mai raka’a biyu ko huɗu da kaifiyyarsa ....................................................... 13